Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dr Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yi kira da a samar da wasu ayyuka na musamman ga mataimakan gwamnoni a kudin tsarin mulkin Nigeria domin su shagaltu da su.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na kungiyar Tsoffin Mataimakan Gwamnonin Najeriya (FFDGN) mai taken: “Hadin kai a cikin manufa daya don samar da shugabanci na gari da ci gaba mai dorewa” a Abuja.

Ganduje, wanda ya samu wakilcin Mista Emma Eneukwu, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, na Kudu, ya bayyana cewa warewa mataimakan gwamnoni ayyuka a kundin tsarin mulkin Nigeria zai hana a samu rikici tsakanin gwamnoni da mataimakansu.
Yadda Wani Saurayi Da Budurwa Suka Daurawa Kansu Aure A Jigawa
“Na yi farin ciki da ku mataimakan gwamnoni, ku ka yanke shawarar hada kanku ta hanyar samar da wata shigifa guda .
“Yayin da kuke wayar da kan jama’a, yayin da kuke ganawa da jama’a kuna tattaunawa da shugabannin kasarmu, akwai bukatar a ba wa kundin tsarin mulkin Nigeria ya baiwa mataimakan gwamnoni aiyuka yi ” inji shi.
