Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano ya sake nada sabbin masu bashi shawara guda 10

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin masu bashi shawara na musamman har guda 10 , a wani ɓangare na cika alkawuran da yayi yakin neman zabe.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.

Talla

Wadanda aka nadan sun hadar da:

1. Hon. Garba Dirbunde, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi

2. Hon. Wakili Aliyu Garko, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kasashen waje

3. Air Commodore Yusha’u Salisu Tudunwada Wada, Rtd. Mai ba da shawara na musamman, akan harkar Tsaro.

4. Hon. Musa Ado Tsamiya, mai ba da shawara na musamman, kan Magudanan ruwa

Talla

5. Gwani Musa Falaki, mai ba da shawara na musamman kan harkokin addini II

6. Dr. Sulaiman Wali Sani, mai ba da shawara na musamman kan harkokin ma’aikatan gwamnati.

7. Farfesa Auwalu Arzai, mai ba da shawara na musamman kan ilimi mai zurfi.

8. Hon. Ahmad Sawaba, mai ba da shawara na musamman kan kula da namun daji.

9. Alh. Tajuddeen Gambo, mai ba da shawara na musamman kan ilimi.

10. Hon. Baba Abubakar Umar, mai ba da shawara na musamman na makarantu masu zaman kansu da na sa kai.

Gwamanan yace an nadasu ne bisa cancanta, aminci da jajircewa wajen yiwa mutanen jihar Kano hidima.

Sanarwar tace nadin nasu ayi shi ne bisa chanchanta sadaukar da kai da kuma la’akari da irin gudunmawar da suka bayar yayin zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...