Mawadata sun taimakawa Marayu a Wannan Sallar – Danlarabawa

Date:

Daga Surayya Abdullah Tukuntawa

Gidauniyar Tallafawa Mabukata daga tushe wato Grassroot Care & Aid Foundation ta rabawa marayu Naman sallah kamar yadda ta sabayi a dukkan shekara a daidai irin wannan lokaci da ake gudanar da Sallah layya.

Gidauniyar ta bawa marayu Naman shanu da raguna Dan suma suyi farin ciki kuma su samu naman da zasuci kamar yadda kowanne gida Iyaye suke Samar da nama ga ‘ya’yansu.

Wannan na kunshe Cikin Wata sanarwa da Shugaban gidauniyar Auwal Muhammad Danlarabawa ya Sanyawa Hannu Kuma ya aikowa Kadaura24.

“Muna godiya ga wani bawan Allah daya bamu Sa, sannan wata baiwar Allah ta Bamu Sa da rago da kuma namu na gidauniya, haka kuma da wadanda suka taimaka da gudunmawarsu na gudanarwa da kukade da akayi hidima kiwo, abinci, fida da Waɗanda Suka taimaka har Naman yaje ga yaran, Allah ya Saka musu da gidan aljannah kamar yadda suka farantawa wadannan yara Rai Allah ya faranta musu suma a rayuwarsu ta duniya da lahira”. Inji Danlarabawa

Shugaban Gidauniyar yace Wannan nama tabbas Yana taimakawa a kowacce shekara idan min fito wannan aiki muna ganin irin yanayin da suke shiga na farin ciki da murna da walwala.

Ya bukaci al’ummar musulmi da su cigaba da tallafawa Gidauniyar domin ta cigaba da taimaka Marayu

16 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...