Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Babban malamin addinin musuluncin nan dake Kano Sheikh Abdulwahab Abdullah ya bukaci talakawa da su guji yiwa mawadaka hassada akan arzikin da Allah ya yi musu.
” Masu kudi ya kamata ku rika bada zakka tare da tallafawa masu karamin karfi saboda tana magance hassada da kiyayya tsakanin mawadata da mabukata”.
Bankwana: Gwamna Ganduje ya nemi afuwar al’ummar jihar kano
Sheikh Abdulwahab Abdullah ya bayyana hakan ne yayin da hukumar zakka ta jihar kano ta rabawa mabukata zakkar bana a gidan gwamnatin jihar kano.
Malamin ya kuma ce bai kamata talakawa su rika yiwa Masu kudi hassada ba saboda Allah ne ya basu, sannan ya bukace su da su rika godewa masu basu zakka da tallafa musu kamar yadda Annabi S A W yayi umarni.
Ya godewa Alh. Aminu Dantata bisa zakkar Naira Miliyan 10 da ya domin rabawa ga mabukata a jihar kano.