Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar Kano KAROTA ta bukaci direbodin jihar da su zamo masu bin doka da oda, a dukkan lokacin da suke kan titunan jihar.
Mataimakin shugaban hukumar Auwal Lawan Aranposu ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar kautar girmamawa da kungiyar shuwagabannin kungiyar direbobin mota ta NURTW shiyyar kano ta kadu ta bashi a dakin taro na hukumar KAROTA dake kano.

Auwal Aranposu ya yabawa kokarin kungiyar na yadda suka ga dacewar bashi wannan kyautar girmama akan yadda yake gudanar da ayyukansa a hukumar
“Yau ina cike da farin ciki, saboda a ko da yaushe kana gudanar da aikin ka tsakaninka da Allah ba domin wani ya yaba maka ba, sai dan ka sauke nauyin da ke wuyanka, kuma kana gwada adalci da jajircewarka akan aikin dake gabanka, kai dai kasan kan yi ne tsakani da Allah”
“Ni bana karbar takardar girmama, idan aka ce za’a karramani nakan ce a bari sai na bar kujerar, anan ne za’a gane cewa na cancanta ko kuma akasin haka”
“Amma a dukkan abin da aka lisafta a wannan waje nasan abubuwa ne da idan an yaba min sakamakon yin su na tabbatar da cewa kwarai na aikata su domin ganin an sami gobe mai kyau a harkokin sufurin jihar kano.”
Da yake jawabi tun da fari Shugaban kungiyar shuwagabannin kungiyoyin direbobin mota ta NURTW shiyyar kano ta kadu Musa Mika’il, ya yabawa Auwal Aranposu bisa yadda yake kokari wajen kari martaba da mutuncin direbon dake yankin Kano ta Kadu dama jihar kano baki daya.
“mai girma DMD bazan cika ka da zance ba ina, illa iyaka an sake mika godiyar mu kan yadda kake kare mutuncin direbobin mu, wannan ce ta sanya a madadin su muka ga dacewar karrama ka da wannan lamba ta girma”.
Taron ya sami halartar daukacin shuwagabannin kungiyar shuwagabannin direbobi ta NURTW shiyyar kano ta kadu.