Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar Najeriya, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Ata, ya nesanta kansa daga wata wasika da ake yadawa a kafafen sada zumunta, wadda ake ikirarin an aike masa da ita, duk da cewa ba ta iso gare shi ta hanyar da ta dace ba.
A wata sanarwa da ya fitar, Ministan ya bayyana mamakinsa kan yadda ‘yan jarida da magoya baya ke tattaunawa kan wasikar kafin ma ta iske shi, yana mai cewa hakan ba daidai ba ne, musamman idan aka yi la’akari da matsayinsa na Minista .
A cewarsa, wasikar ma ba ta ƙunshi takamaiman tuhumar da ake yi masa ba, a saboda haka, ya ce babu wani dalili da zai sa ya mayar da martani kan abin da bai da tushe balle makama.

Ata ya jaddada cewa yana da cikakken ‘yancin fadin albarkacin bakinsa bisa tanajin kundin tsarin mulki, kuma bai taɓa yin wata magana kai tsaye ko a kaikaice da ke nuna tilasta ra’ayi, ko goyon bayan wani mutum a madadin jam’iyya ba.
“Bugu da ƙari, wasikar ba ta ambaci wata takamaimiyar magana, aiki, ko abun da ake zargi na da aikata wa ba. “Shima kuma gargadin da aka ambata kan abinda ake zargi na dashi gaba ɗaya babu bukatar mayar da martani akai”. Inji Ata
APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu
“Don haka, a matsayi na na ɗan Najeriya, ina da cikakkiyar dama da iko wanda kundin tsarin mulki ya bani na bayyana ra’ayoyi na na kashin kai na. Ban taɓa wani ikirari kai tsaye ko a kaikaice na cewa sai an bi wane, ko dole abi ra’ayin wane a madadin jam’iyya ba, sam sam. Duk maganar da zan yi, ina yin ta ne a matsayi na na mutum mai cikakken iko”. Inji Minista Ata
Haka kuma, ina da iko da damar ci gaba da yada manufofi masu amfani da kuma tsarin Renewed Hope na shugaban kasa. Na kasance mai kare martaba da muhibba ta shugaban kasa kuma babban Kwamandan Rundunonin Najeriya, mai girma Bola Ahmad Tinubu, GCFR, kuma zan ci gaba da yin hakan cike da aminci da biyayya.
Har yanzu ina nan a matsayin mamba nagari mai biyayya ga jam’iyyarmu ta APC, kuma ina ƙoƙari wajen yadawa tare da aiwatar da ayyukan cigaban al’umma da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ke aiwatarwa, domin amfanin jam’iyyar tamu da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya.
Ministan ya ce “Ina fatan za a karbi wadannan bayanai nawa cikin mutuntaka da kuma girmamawa.