APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Date:

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi Abbas ta yi wa Ministan Gidaje na Tarayya, Hon. Yusuf Abdullahi Ata, gargadi kan wasu maganganun da yake furtawa game da harkokin cikin gida na jam’iyyar da ‘yan takara a cikin APC.

Ida dai za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a yan kwanakin nan Minista ata yana yawon shiga kafafen yada labarai yana tallata manufar Sanata Barau Jibrin ta Neman takarar Gwamnan Kano a zaben 2027.

A cewar wata wasiƙa da Mai dauke da sa hannun Shugaban jam’iyyar na jihar Kano Abdullahi Abbas, wadda aka aikewa Ata ta nuna waɗannan kalamai suna da yiwuwar haifar da rikici, rashin fahimta, da rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

InShot 20250309 102512486

Wasiƙar ta kuma bayyana cewa Minista Ata ba shi ne mai magana da yawun jam’iyya ba, don haka kalamansa ka iya rikita jama’a su ɗauka abun da yake fada matsayar jam’iyyar ce.

An tunatar da shi cewa matsayin sa na Babban jami’i a gwamnatin tarayya ya na buƙatar ya rinka furta maganganu masu ƙarfafa haɗin kai a cikin APC.

Shugaban APC Kano, Abdullahi Abbas, ya ce jam’iyyar ta lura Ministan na yawan yin maganganu marasa kamun kai, sannan ta gargade shi ya daina, ko kuma jam’iyyar ta ɗauki matakin ladabtarwa.

Bayan aika masa da Wasikar, Jam’iyyar APC ta kuma turawa Shugaban Kasa Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar na Kasa da Ofishin jam’iyyar na Arewa maso yammacin Nigeria wasikar domin su shaida matsayar jam’iyyar ta APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...

NUC ta kakabawa jami’o’i takunkumi kan yadda suke ba da digirin girmamawa a Najeriya

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta sanar...

Tsoffin Kwamishinonin Kano sun Musanta labarin goyon bayan Sanata Barau a 2027

Kungiya ta tsoffin kwamishinoni da suka yi aiki a...