Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta sanar da sabbin matakai domin dakile yadda ake ba da digirin girmamawa ba bisa ka’ida ba, ciki har da haramta bai wa duk wani jami’in gwamnati mai rike da mukami irin wannan digiri.
Shugaban Hukumar NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Juma’a yayin da ya karɓi rahoton kwamitin da aka dorawa alhakin binciken yadda ake bayar da digirin girmamawa da kuma yadda masu karɓa ke amfani da su .

Farfesa Ribadu ya ce hukumar ta shiga lamarin ne bayan binciken da aka gudanar a fadin ƙasa kan hanyoyin da ake bi wajen bayar da digirin girmamawa da yadda ake amfani da shi.
“An samar da waɗannan digirgir ne domin karrama mutanen da suka yi abin a-zo-a-gani, amma abin bakin ciki shi ne yadda aka fara karkatar da manufar zuwa wani abun na daban,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa matsalar ta ta’azzara sakamakon yawaitar makarantu na bogi da waɗanda hukumomi na cikin gida da na waje ba su aminta da su ba kuma suka mayar da digirin girmamawa tamkar kasuwanci.
Solacebase