‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

Date:

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya.

‎Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya.

‎A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro.
InShot 20250309 102512486

‎Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da kuma kauce wa duk wata barazana.

‎Makarantun da abin ya shafa sun haɗa da waɗanda ke Zariya, Daura, Sakkwato, Potiskum, Ikare-Akoko, Abaji, da sauransu.

‎Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren da ake kai wa makarantu ke ƙara tsananta.

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NUC ta kakabawa jami’o’i takunkumi kan yadda suke ba da digirin girmamawa a Najeriya

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta sanar...

Tsoffin Kwamishinonin Kano sun Musanta labarin goyon bayan Sanata Barau a 2027

Kungiya ta tsoffin kwamishinoni da suka yi aiki a...

Kungiyar Iyayen Daliban MAAUN Ta Karyata Koken da Aka Kai wa PCACC, Ta Ce Jami’ar Na Da ‘Yancin Kanta

Shugaban Kungiyar Iyayen daliban  jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe,...