Shugaban Kungiyar Iyayen daliban jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe, ya yi watsi da rahotannin kafofin watsa labarai da ke zargin cewa jami’ar ta kakaba kudin yaye dalibai mai tsada sosai.
A wata sanarwa da ya fitar tare da sa hannun Sakataren kungiyar, Hajiya Habiba Sarki, ya bayyana koken da aka shigar da kuma rahotannin da suka biyo baya a matsayin neman bata sunan jami’ar ba tare da wata hujja ba.
“MAAUN na daya daga cikin jami’o’in kudi masu sauƙin farashi a Kano, tana ba da ingantacciyar ilimi tare da kayatattun gine-gine. Wasu jami’o’in kudi a jihar suna cajin kudin makaranta ninki uku a kan na MAAUN, amma ba a jin kukan kowa game da su. Me ya sa sai MAAUN ake nufi?

“Idan dalibi ya biya kudin makaranta na tsawon shekaru hudu, me ya sa za a ga laifi idan aka nemi ya biya kudin yayewa a jami’a mai zaman kanta? Wannan ba wani sabon abu bane. Wannan batu gabaɗaya na nuna wata makarkashiya ce da nufin bata suna da barazana daga wani ba a san ko waye ba da yake ikirarin cewa yana kare muradun dalibai da iyaye.
Me ya hada MAAUN da Hukumar Karɓar Korafe-Korafe ta al’umma (PCACC) a wannan lamari?” in ji shi.
Ya kuma shawarci wanda ya kafa jami’ar da ya ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantaccen ilimi, yana yaba masa bisa kishin kasa da jajircewa wajen barin kudin makaranta yadda yake duk da matsin tattalin arzikin da ya tilasta wasu jami’o’i da dama kara kudinsu.