Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yaba da hukuncin kotun Majistiri da ya umarci hukumar ta daura aure tsakanin ‘yan Tiktok din nan guda biyu, Ashiru Mai Wushirya da ‘Yar Guda.
Mataimakin Babban Kwamandan hukumar na jihar Kano, Dakta Mujahideen Aminudeen ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa manema labarai.
Acewar, Mujahideen Aminudeen hukuncin ya yi daidai duba da yadda hukumar ta Hisbah ke yaƙi da aikata badala da abubuwan da suka sabawa al’ada da addini.
Sannan Malamin ya ce za a sanya su cikin shirin auren Gata da hukumar za ta aiwatar bisa sahalewar Gwamnatin jihar.
RMK@69: Tinubu ya yi wa Kwankwaso kyakykyawan yabo
“Mai girma babban kwamanda ya bada tsarin aure da ake yi guda biyar waɗanda dukkan su an yarda dasu an amince dasu, za a tuntubi iyayensu domin su amince. Tuni Babban Kwamandan ya tura Zamfara domin a binciko iyayenta a tawo dasu, domin su zasu wakilce ta.”
Malamin ya ce Kuma tuni aka yi musu gwaji na Kwakwalwa saboda shaye-shaye kuma za a duba lafiyarsu domin a gudanar da Auren.
Sannan ya ce Auren zai zama “Mutu Ka Raba” domin hukumar ba zata amince da saki ba.
Haka kuma, ya ja hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta su guji yin wasa da aure domin Sunnah ce ta Manzon Allah Sallallahu Alayhi Wassalam.