Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na kammala manyan ayyukan gine-gine da nufin inganta walwalar jama’a.
Kwamishinan Sashen Kula da Ayyuka, Nura Ma’aji, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Talata, bayan duba wasu ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa a fadin jihar.
A cewar sa, aikin gina gadar sama ta Dan’Agundi da ta Tal’udu zai kammalu kafin karshen watan Disamba.
Ma’aji ya ce an riga an biya diyya da warware duk wasu batutuwan da suka shafi aikin domin tabbatar da kammalawarsa a kan lokaci.
Ya bayyana cewa ana gudanar da binciken aiki a kai a kai domin tabbatar da inganci da saurin ci gaba, tare da jaddada cewa wadannan gadaje za su taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a birnin Kano.
Kwamishinan ya kara da cewa an tsara kaddamar da ayyukan a watan Janairu 2026 a matsayin wani bangare na shirin gwamnatin jihar na ci gaban kayayyakin more rayuwa.
Ya bukaci goyon bayan jama’a domin ganin an cimma manufofin gwamnati yadda ya kamata.