Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya kaddamar da Kwamitin Kula da Harkokin Jiragen Sama na aikin Hajjin shekara ta 2026 a ofishin hukumar dake Abuja.
Yayin kaddamar da kwamitin, Farfesa Usman ya ce an kafa kwamitin ne domin tabbatar da tsabtaccen aiki da bin doka a duk harkokin da suka shafi jigilar alhazai ta jiragen sama. Ya bayyana cewa gwamnati karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki hidimar alhazai a matsayin amanar da ba za ta yi wasa da ita ba.
Ya ce duk da cewa an samu ci gaba a bangaren jigilar alhazai a shekarun baya, hakan ba zai sa suyi Kasa a gwiwaba saboda muhimmancin da bangare ke da shi a aikin Hajji.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ayyuka na hukumar, Prince Anofi Elegushi, ya gode wa shugaban hukumar bisa amincewa da kwamitin, yana mai tabbatar da cewa za su yi aiki tukuru don ganin alhazai sun yi tafiya cikin tsaro da girmamawa.
Ayyukan kwamitin sun haɗa da:
Duba takardun kamfanonin jiragen sama masu neman aiki da NAHCON.
Kula da shirye-shiryen filayen jiragen sama kafin aikin Hajji.
Sa ido kan tashin jiragen alhazai da saukarsu.
Tabbatar da bin ka’idojin jigilar kaya da dokokin hukumar.
Ba da rahoto ko shawarwari kan duk wata matsala da ta taso.
Farfesa Usman ya yi kira ga mambobin kwamitin da su yi aiki bisa gaskiya, kishin kasa da kwarewa, yana mai tunatar da su cewa idanuwan miliyoyin yan Nigeria na kallon aikinsu.