Gwamnonin Kano Katsina da Jigawa sun shiga yarjejeniyar da wani kamfanin makamashi

Date:

Gwamnonin Kano da Katsina da kuma Jigawa sun shiga yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa kasuwar wutar lantarkin jihohin uku tare da zuba hannun jari a kamfanin Future Energies Africa (FEA), babban mai zuba jari a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano wato KEDCO.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na jihar Kano, Dr. Gaddafi Sani Shehu ya fitar.

Sanarwar ta ce an cimma wannan yarjejeniyar ne yayin wani taro kan bunƙasa lantarki da aka gudanar a birnin Marrakech, Morocco, daga ranar 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025.

Dr. Gaddafi ya ce jihohin uku za su yi aiki tare wajen gano hanyoyin da za su amfanar da kasuwannin wutar lantarkinsu, tare da kafa tsare-tsaren doka da hadin gwiwa domin inganta aiki.

Ya kara da cewa “samun hannun jari a kamfanin FEA zai taimaka wajen karfafa dabarun KEDCO da kuma haɓaka rarraba wutar lantarki a yankin Arewacin Yamma.”

Kwamishinan ya bayyana cewa “Za a kafa asusun naira 50 biliyan na wutar lantarki domin hanzarta samar da wuta ga al’umma ta hanyoyi da dama kamar samar da wuta a gida da tsarin hasken rana da sauransu.”

“Haka zalika, za a yi aiki tare da KEDCO domin rage asarar wutar lantarki daga masu amfani da lantarkin a gida, wanda zai tabbatar da ingantaccen samar da wuta ga al’umma.”

An tsara cewa wakilan jihohin za su gudanar da taron kasa da kasa a kowace shekara, sannan su gana sau huɗu a shekara domin duba ci gaban ayyuka da tsara manufofi da karfafa dangantaka a kasuwar wutar lantarki ta jihohi uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

RMK@69: Kwankwaso Jagora Ne Mai Hangen Nesa, Abba Kuma Na Kawo Ci Gaba a Kano – Bakwana

Wani jigo a kungiyar Kwankwasiyya, kuma tsohon mai ba...

Da dumi-dumi: Tinubu ya nada sabon Minista

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan...

Kashim Shattima ya sauka daga kujerar ta mataimakin shugaban Nigeria ya baiwa wata yarinya

Mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima ya sauka daga kujerarsa...

Gwamnatin Kano ta baiyana lokacin da za ta kammala aikin gadojin sama na Tal’udu da Dan’Agundi — Kwamishina

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na kammala...