Kotu Ta Dakatar da ‘Yan Sanda Daga Tilastawa Masu Motoci Mallakar Izinin Amfani da Gilashin Mota Mai Duhu

Date:


‎Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Warri, Jihar Delta, ta bayar da umarni ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa (IGP) da su dakatar da yunkurisu na tilastawa masu motoci mallakar izinin amfani da gilashin mota mai duhu.

‎Kotun ta umarci ‘yan sanda da IGP da su tabbatar su bi doka da kuma mutunta tsarin shari’a har sai an kammala sauraron ƙarar da ke gaban ta.


‎Wannan umarni na wucin-gadi ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/WR/CS/103/2025, wadda lauya John Aikpokpo-Martins ya shigar gaban kotu, inda ya kalubalanci sahihancin tilasta sabuwar dokar lasisin gilashin mota mai duhu.

‎A cikin hukuncin, kotun ta jaddada cewa ya zama dole ga hukumomin ‘yan sanda su girmama tsarin shari’a kafin a ɗauki wani mataki na gaba kan batun.


‎Barrister Kunle Edun, SAN, wanda ya jagoranci tawagar lauyoyin mai ƙara, shi ne ya tabbatar da wannan ci gaban ga manema labarai, inda ya ce wannan umarni na kotu babban ci gaba ne wajen tabbatar da bin doka yayin da ake jiran kammala sauraron shari’ar gaba ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...