Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar da sakamakon jarrabawar wannan shekara ta 2025.
Sakamakon ya nuna cewa kashi 60.26 cikin 100 na waɗanda suka samu kiredita biyar zuwa sama ciki har da darussan Lissafi da Turanci.

Shugaban hukumar Farfesa Ibrahim Wishishi ya shaida wa BBC cewa jihar Kano ce kan gaba a yawan ɗaliban da suka samu nasara a jarrabawar a faɗin wuraren da hukumar ke shirya jarrabawar da suka haɗa da wasu ƙasashen Afirka.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin Kanon ta fitar ta ce wannan ne karon farko cikin shekara 25 da jihar ta samu wannan nasara.
Shugaban na NECO ya ce cikin ɗalibai 1,358,339 da suka rubuta jarrabawar, yayin da 818,492 ne suka samu kiredit a darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.