Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana damuwa kan yadda talauci ke ci gaba da addabar al’umma a matakin ƙasa, duk da makudan kudaden da ake rarrabawa ga Kananan hukumomi daga gwamnatin tarayya.
Yayin wata hira da aka yi da shi kai tsaye, Sanata Kawu ya ce Kananan Hukumomi 44 na jihar Kano sun karɓi jimillar kudin da suka kai Naira biliyan 130.74 daga watan Janairu zuwa Yuni, 2025. Sai dai, ya ce al’umma ba sa ganin tasirin kudaden saboda rashin cikakken ‘yancin cin fashin kan kananan hukumomin.
Ya ce a matsayinsa na dan Kasa ya rubutawa ofishin akanta Janar na kasa, bukatar a bashi bayanan kudaden da aka turawa kananan hukumomin jihar Kano .
Ga kuma bayanin kudaden da aka tura kananan hukumomin jihar Kano .
Kananan Hukumomi 15 na Kano ta Tsakiya sun karɓi Naira biliyan 49.42.
Kananan Hukumomi 16 na Kano ta Kudu sun samu Naira biliyan 45.46.
Kananan Hukumomi 13 na Kano ta Arewa sun karbi kudin da suka kai Naira biliyan 35.87.
Ya ƙara da cewa: “ Karamar Hukumar Nassarawa ita ce ta fi karɓar kudi Mai yawa inda aka bata Naira biliyan 5.12, yayin da Tofa ta karɓi mafi ƙanƙantar kudin da suka kai Naira biliyan 2.34.”
Sanata Kawu ya bayyana cewa matsalar ba ta tsaya ga Kano kaɗai ba, domin ko a sauran jihohi, an samu karuwar kaso tsakanin 95 zuwa 125% a rarraba kudaden Kananan Hukumomi idan aka kwatanta da shekarar 2023.
Sai dai ya ce duk da wannan karin kudi, matsalolin rashin aikin yi, karancin kudaden K ula da kiwon lafiya, makarantu da ke fama da rashin kayan aiki da kuma talauci ba su ragu ba.
Ra’ayi:Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello
A cewarsa, Kananan Hukumomi suna samun kudaden shiga na cikin gida da kuma tallafi daga kungiyoyi da kuma gudummawar masu ruwa da tsaki, abin da zai iya inganta rayuwar al’umma idan aka barsu su sarrafa kudaden su da kansu.
Ya ce: “Ku yi tunanin idan Kananan Hukumomi suna da ‘yancin sarrafa kudadensu kai tsaye – za su iya ɗaukar matasa aiki, za su iya baiwa ‘yan kwangila na cikin gida damar yin ayyuka, farfaɗo da kasuwanni, ba da tallafin gaggawa idan aka Sami wata matsala, da kuma inganta makarantu da asibitoci. Amma saboda rashin ‘yancin kai, kudaden suna ga makalewa su kuma al’umma suna cikin mawuyacin hali.”

Sanatan, wanda tsohon hadimin shugaban kasa ne, ya bayyana cewa batun bayar da ‘yancin kai ga kananan hukumomi tun tuni ya kamata a aiwatar da shi.
Ya kuma yi kiran gaggawa ga gwamnati da ta aiwatar da sauye-sauye domin tabbatar da ‘yancin kudi da gudanarwa ga kananan hukumomi.
A cewarsa: “Rashin yin hakan, kananan hukumomi za su ci gaba da zama a yadda suke duk kuwa da makudan kudaden da ake tura musu daga Asusun gwamnatin tarayya.