Ra’ayi:‎Tsarin Kwankwasiyya ya dora Kano a gwadaben cigaba a mulkin Gwamna Abba Kabir -Adamu Shehu Bello

Date:


‎Ra’ayi

‎Daga Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi), Jigo a Kwankwasiyya kuma PRO na Kasuwar Dawanau

‎Tun daga ranar da ya hau kujerar mulkin kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kansa a matsayin shugaba mai hangen nesa, jarumtaka da tausayi, Wanda yake gudanar da harkokinsa bisa tsarin Kwankwasiyya na sadaukarwa, gaskiya da hada kai, wanda ya mayar da Jihar Kano sabuwa. Gwamnatin sa na karkata ne kan jama’a, da akidar cewa gwamnati dole ta tabo rayuwar talakawa kai tsaye.


‎Sauya Fasalin Ilimi

‎Daya daga cikin manyan nasarorin da  Gwamna Abba Kabir  Yusuf ya samu har da har fannin ilimi. Bayan ya ayyana dokar ta baci kan ilimi, ya fara gyaran makarantun da suka lalace, da samar da kayan aiki a ajujuwa tare da daukar kwararrun malamai. Wannan yunkuri ya dawo da martabar makarantun gwamnati, tare da tabbatar da cewa kowanne yaro a Kano yana samun ingantaccen Ilimi ba tare da la’akari da inda ya fito ba. Mu a Kwankwasiyya, ilimi ginshiki ne na inganta rayuwar al’umma, kuma matakan Gwamna Yusuf na nuni da cewa ‘ya’yanmu za su sami ingantacciyar rayuwa.


‎Lafiya Ga Kowa

‎Haka zalika, a bangaren lafiya gwamnatin Abba Kabir  Yusuf ta dauki matakai masu muhimmanci. Ta gyara asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko tare da samar musu da kayayyakin aiki na zamani. Wannan mataki ya tabbatar da yadda gwamnan ya damu da harkar kiwon lafiya, inda talakawa ke samun damar kula da lafiyarsu cikin sauki da rangwamen kudi. Wannan ba wai kawai ya ceto rayukan al’umma bane, har ma ya rage yawaitar kamuwa da cututtuka a jihar Kano .

‎Tallafa wa Kasuwanci da Sana’o’i

‎A matsayina na dan kasuwa a Kasuwar Dawanau babbar kasuwar hatsi a Afirka ta Yamma, ina iya shaida canjin da Gwamna Yusuf ke kawowa a fannin kasuwanci. Manufofinsa na saukaka harkokin cinikayya, Samar da ababen more rayuwa da kuma karfafar kananan masana’antu, inda ake samun taimakekeniya tsakanin manoma da ‘yan kasuwa. Ta hanyar ba matasa ‘yan kasuwa damar yin gogayya da takwarorinsu, gwamnan ya rage zaman banza a tsakanin Matasa.

‎Gina Jama’a, Ba Gina Gine-gine Kadai Ba

‎Baya ga manyan ayyukan gine-gine, Gwamna Yusuf na saka hannun jari a cikin jama’a. Shirinsa na tallafawa mata, koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai da kuma yaki da miyagun dabi’u na nuni da cikakken hangen nesa na gwamnan a  mulkinsa. Ya fahimci cewa ci gaba ba gina tituna ko gadajensu bane kawai, har da  gina mutune su kuma su gina Kasa.


‎Dawo da yarda tsakanin gwamnati da Jama’a

FB IMG 1753738820016
Talla


‎Babban abun murnar shi ne yadda gwamna Abba ya dawo da yarda tsakanin gwamnati da al’umma. Tsawon shekaru, mutane sun fidda tsammani ga gwamnati, amma A yau, Gwamna Yusuf na karbar shawarwari, da sauraren koken al’umma, sannan yana daukar matakai bisa Irin Wanda al’umma suke so, wannan yasa al’ummar Kano sun sami kwarin gwiwa da amincewa cewa gwamnati na iya yi wa jama’a abun da suke so.

‎Manufar Kwankwasiyya Aiki

‎Wadannan nasarori dukkansu na nuni da cigaban da tsarin Kwankwasiyya ta kawo, wanda aka gina a kan sadaukarwa, ladabi da hidima ga jama’a. Kwankwasiyya ba ta alfarma bace, illa dai amfani da iko don daukaka talakawa da tallafawa marasa galihu. Gwamna Abba Kabir Yusuf a yau shi ne tamkar ainihin fassarar wannan akida, wanda muke fata ya zamewa matasa abin koyi.

‎A madadin mabiya Kwankwasiyya da al’ummar Kasuwar Dawanau, ina sake jaddada goyon bayanmu mara iyaka ga Gwamna Abba Kabir Yusuf. Muna kira gare shi da ya ci gaba da tsayawa kai da fata, ya dore kan wannan tafarki. Da hadin kai, addu’a da jajircewa, Jihar Kano za ta cimma manyan manufofi kuma ta zama abin koyi a tsarin mulki nagari a Najeriya.

‎Adamu Shehu Bello (Bayero Chedi)
‎Jigo a Kwankwasiyya kuma PRO na Kasuwar Dawanau

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kamata ya yi wajen Mauludi ya Zama waje Mai nutsuwa saboda ana ambaton Allah da Manzonsa – Mal Ibrahim Khalil

Shugaban Majalisar shuhurar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam...

Al’ummar Garin Riruwai da wani Kamfanin Hakar ma’adanai Sun Cimma Yarjejeniya Kan Ci gaban yankin

Kwamitin ci gaban Al’ummar garajn Riruwai da wani kamfanin...

Sarkin Daura ya nuna inda za’a binne shi idan ya rasu.

  Mai Martaba Sarkin Daura dake jihar katsina Alhaji Dr....