Mai Martaba Sarkin Daura dake jihar katsina Alhaji Dr. Faruk Umar Faruk ya nuna inda za’a binne shi idan ya rasu.

Sarkin ya bayyana hakan a ya yin da yake tare da tsohon Gwamnan Jigawa, Dr. Sule Lamido da Janar Aliyu Gusau Rtd da Alhaji Dahiru Barau Mangal, ajiyan Katsina da sauran wasu muhimman mutane, inda yake nuna musu kabarin marigayi Sarki Muhammad Bashar da na Sarki Abdurrahman da Sarki Mallam Musa, wadda suke waje kuma Sarakunan Fulani ne da suka mulki Daura.
A nan ne Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk ya nuna musu inda za a binne shi idan ta Allah ta kasan ce.
An gabatar da addu’oi na musamman na neman Allah ya jikansu da rahama ya gafarta musu ya kyautata makwancin dukkan musulmi.
Arewa Radio