Majalisar ƙaramar hukumar Gwarzo ta amince da ware sama da naira miliyan 31 domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da ke karatu a jami’o’i daban-daban a cikin gida da kuma ƙasashen waje.
Shugaban ƙaramar hukumar, Dakta Mani Tsoho, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi wakilan ƙungiyar ɗalibai mai suna Gida Gida Scholars a ofishinsa ranar Litinin.
Dakta Tsoho ya bayyana godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa wannan kyakkyawan shiri, inda ya roƙi ɗaliban su kasance jakadun jihar Kano na gari da kuma ƙaramar hukumar Gwarzo a duk inda suke karatu. Ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnatin ƙaramar hukumar za ta ci gaba da tallafa musu don sauƙaƙa musu a harkokin karatunsu .
Za mu yi Aiki ba Dare ba Rana domin Tabbatar da Umarnin da Ganduje ya ba mu Baffa Babba Dan’agundi
A jawabin da shugaban ɗaliban ya gabatar a madadinsu, ya bayyana cewa ziyarar nasu ta kasance ne domin gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da kuma shugaban ƙaramar hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho, bisa wannan tallafi mai muhimmanci. Ya kuma yi alkawarin cewa za su kasance wakilai nagari na jihar Kano a makarantunsu.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na shiyyar Gwarzo Auwalu Musa Yola ya a fitar , ya ce Shi ma sakataren ƙaramar hukumar Gwarzo, Alhaji Sunusi Abdullahi Getso, ya shawarci ɗaliban da su kasance jakadu nagari na Gwarzo da jihar Kano, tare da nisantar miyagun ƙungiyoyi da shaye-shaye.