Al’ummomin unguwannin Danbare, Hawan Dawaki, Kuyan Ta Inna, Gwazaye da Yammawa sun yi kira ga hukumomi da su kawo dauki cikin gaggawa kan yunkurin da wasu mutane ke yi na kwace filin makarantar gwamnati a yankin Kuyan Ta Inna.
Mutanen yankin sun bayyana damuwarsu ne bayan da wasu suka fara gina gine-gine a kan wasu filaye da aka ware tun da farko domin asibiti da masallaci, sannan suka karkata hankalinsu zuwa filin makaranta.

A cewar mazauna yankin, hakan barazana ce ga makomar ilimi da cigaban al’ummar yankin.
Shugaban kwamitin ci gaban yankin, Baba Habu Miika’ilu Warure, ya ce wannan lamarin ya haifar da fargaba mai tsanani a tsakanin iyaye da yara, domin rashin makaranta a yankin zai jefa su cikin babban kalubale.
Da yake karin bayani, shugaban karamar hukumar Kumbotso, Hon. Abdullahi Ghali Basaf, ya tabbatar da cewa sun karbi korafin jama’a, kuma tuni an dauki matakan dakile yunkurin kwace filin.
“Muna da niyyar gina makaranta a filin domin kare hakkokin al’umma. Ba za mu lamunci duk wani yunkuri na kwace filayen da aka ware musu ba,” in ji shi.