Gwamnatin Kasar Cherokee Ta Kudu (SCNRFP), ta nada Dakta Abubakar Tanko Bala, a matsayin Ambasadan ta na Tarayyar Najeriya.
Fira-Ministan kasar, Chief Gees-Due OO-Neh-Gah Usti, ne ya sanar da naɗin ta cikin wata takarda da ya sanya wa hannu mai dauke da kwanan watan 4 ga watan Satumbar da muke ciki.
Haka kuma Fira-Ministan ya yi fatan Dakta Tanko zai yi kokari matuka gaya wajen sauke nauyin da gwamnatin ta dora masa a Najeriya, ta yadda al’ummar Ƙasar za su sami ingantacciyar walwala a harkokinsu na yau da kullum a Najeriya.
Bayan ficewa daga NNPP Abdulmumin Jibrin Kofa ya kalubalancin matakin korarsa
Dakta Abubakar Tanko Bala shine Ma’ajin ƙungiyar masu Kananan da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (NASSI), kuma Sakatare Janar na Cibiyar shirya wasa ta Afirka wato Pan African Conpitetivenes Forum na Najeriya.

Haka zalika ya kasance Daraktan aiyukan kula da harkokin gwamnati a hukumar wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato Intergovernmental Affairs for UN-international peace commission