CSOs sun yi Zanga-Zangar Adawa da Rashawa kan Zargin Satar Naira Biliyan 6.5 a Ofishin DG Protocol na Kano

Date:

Kungiyar Kare Muradun Jama’a na Kano (CSOs Against Corruption) sun gudanar da zanga-zanga tare domin nuna goyon baya ga hukumar EFCC da ICPC a yunkurinsu na yaki da rashawa a jihar.

Kungiyoyin sun bayyana cewa zanga-zangar ta zama hanya ta jan hankalin hukumomi kan bukatar daukar matakin gaggawa wajen tabbatar da gaskiya da adalci tare da kare dukiyar jama’a.

Zargin Rashawa Kungiyoyin sun nuna damuwarsu kan yadda hukumar EFCC da ICPC suka fallasa zargin karkatar da kudaden jama’a har Naira biliyan 6.5 da ake zargin Daraktan Jana dake Kula da al’amuran gwamnan na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Rogo, ya yi. Sai dai duk da hukumar ICPC ta ce ta karbo sama da Naira biliyan 1.2 daga cikin kudaden, gwamnatin jihar ta karyata rahoton tare da yin kokarin kawar da hankalin jama’a daga gaskiyar al’amari.

Kungiyoyin sun ce wannan batu ba shi kaɗai bane, domin daga shekarar 2023 zuwa 2025, Kano ta samu fiye da Naira biliyan 445 daga gwamnatin tarayya ban da kudaden shiga na cikin gida. Duk da haka, asibitoci sun lalace, makarantu sun rufta, hanyoyi sun baci, ruwa ya gagara, talauci kuma ya yi katutu.

Manyan Badakalar da Aka Bankado
An karkatar da tallafin kayan abinci da gwamnatin tarayya ta turo domin talakawa, inda aka samu tirelolin shinkafa, masara da taki a ma’ajiyoyin ‘yan siyasa da jami’an gwamnati.
Badakalar magunguna ta Novomed inda aka biya kudaden magunguna ga kananan hukumomi amma ba a kawo ko kwandon magani guda ba.

Badakalar kwangilar aikin gona (ACRISAL) da aka ce an yi almundahana da daruruwan miliyoyin naira.

Shirin tallafin mata da aka ware N50,000 ga kowacce, amma aka karkatar da kudaden.

FB IMG 1753738820016
Talla

Ayyukan hanyoyin cikin birni da aka kashe sama da Naira biliyan 4 amma aka gina hanyoyi marasa inganci.

Tallafin kayan abinci da aka sake jefawa cikin gidajen wasu jami’an gwamnati da suka yi yunƙurin sake siyarwa.

Matsayar Kungiyoyin

Kungiyoyin sun bayyana cewa idan kudaden da ake zargin an karkatar da su da gaske aka yi amfani da su yadda ya dace, da tuni an:

Samar da ruwan sha a dukkan kananan hukumomi 44.

Gyara da fadada makarantu tare da biya wa dalibai kudin jarabawar WAEC/NECO/JAMB.

Gina sabbin asibitoci da na’urori a muhimman kananan hukumomi.

Gina hanyoyi da gadar sama don rage karuwar laifuka.

Bukatun Kungiyoyin Kungiyoyin sun yaba da kokarin EFCC da ICPC tare da bukatar su ci gaba da shari’ar har sai an tabbatar da gaskiya.

Su guji karbar cin hanci ko matsin lambar siyasa daga gwamnatin Kano.

A dawo da dukiyar da aka sace sannan a yi amfani da ita a gaban jama’a.

Majalisar dokokin jihar ta kafa kwamiti na musamman domin bincike.

Kotuna su tabbatar da gaskiya ba tare da son kai ba.

Kungiyoyin sun la’anci gallazawa ‘yan jarida da masu rajin farar hula da ake yi a jihar.
Kiran Ga Jama’a.

Kungiyoyin sun yi kira ga al’ummar Kano da su tashi tsaye wajen yaki da rashawa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba, domin batun ya shafi makomar jihar da ‘ya’yanta.

Kungiyoyin sun kammala da kiran:

Kudin Kano na ’yan Kano ne!

A kawo karshen rashawa!

A tabbatar da gaskiya da adalci yanzu!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...