Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano ta Fitar da Kudin Ajiya da Adadin Kujerun Hajji na 2026

Date:

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya sanar da kudin ajiya na aikin Hajji na shekarar 2026 bisa umarnin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON).

Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana hakan ne yayin taro da mambobin hukumar, jami’an gudanarwa, da kuma jami’an Alhazai na kananan hukumomi a ofishinsa.

Ya ce NAHCON ta amince da naira miliyan takwas da rabi (₦8,500,000) a matsayin kudin ajiya ga duk mai niyyar zuwa aikin Hajji a shekarar 2026. Hukumar za ta karɓi kudaden ne ta hanyar banki ta hannun jami’an Alhazai na kananan hukumomi.

Shugaban K/H Dala da na Legal za su fuskanci tambayoyi a hukumar yaki da rashawa ta Kano

Haka kuma, Alhaji Lamin ya bayyana cewa Jihar Kano ta samu kujeru 5,684 don aikin Hajji na 2026. Ya ce an fara karɓar kudaden ajiya daga yanzu, kuma za a ci gaba da karɓa har zuwa 5 ga Oktoba, 2025, ranar da za a fitar da cikakken kudin aikin Hajjin 2026.

FB IMG 1753738820016
Talla

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya aikowa Kadaura24 ya ce, Shugaban hukumar ya shawarci duk masu niyyar zuwa aikin Hajji su gaggauta biyan kudaden ajiya domin bin jadawalin da Saudiyya ta tanada. Ya kuma jaddada cewa dole ne duk mai neman zuwa aikin Hajji ya kawo hotuna guda takwas (passport size) da fasfo na ƙasa da ƙasa mai inganci.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya yi addu’a ga Allah ya ba wa duk masu niyyar zuwa aikin Hajji damar biyan kuɗin cikin sauƙi. Ya kuma umarci jami’an Alhazai na kananan hukumomi da su yi aiki tukuru wajen tabbatar da cewar kowace karamar hukuma ta samu kujerun da aka ware mata yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...