Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro ya musanta zargin da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi cewa gwamnati na biyan kuɗi da bayar da wasu abubuwa ga ’yan bindiga domin samun zaman lafiya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ofishin, Zakari Mijinyawa, ya fitar daren Lahadi, ofishin ya ce, “wannan zargi ba shi da tushe. Babu wani lokaci da ONSA ko wata hukuma a ƙarƙashin wannan gwamnatin ta shiga harkar biyan fansa ko ba wa masu laifi tallafi. Akasin haka, mun sha gargadin ’yan Najeriya da kada su biya fansa. Zargin El-Rufai ƙarya ne kuma ya saba wa hujjojin da ake iya gani a kasa.”
Sanarwar ta bayyana cewa tun daga farko, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauki dabaru biyu a lokaci guda: gudanar da ayyukan soji da ƙarfin iko tare da tattaunawa da al’umma domin magance ƙorafe-ƙorafen cikin gida.
A cewar ofishin da Nuhu Ribadu ke jagoranta, wannan tsari ya samar da sauƙi a wurare kamar Igabi, Birnin Gwari, da Giwa a Jihar Kaduna, waɗanda a da suka sha fama da hare-haren ta’addanci, amma yanzu suna samun ɗan zaman lafiya.

Ofishin ya kuma jaddada cewa an samu nasarori masu yawa wajen kamawa da kawar da manyan shugabannin ’yan bindiga a jihar. Inda sanarwar ta ce, a Kaduna kaɗai, an hallaka ko kama shahararrun masu ta’addanci kamar Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari da Boka, tare da kama shugabannin kungiyar Ansaru da suka kafa sansanoni a yankin.
Sai dai ONSA ta ce wannan nasara ta zo da asara, domin wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu a yayin fafatawa. “Don tsohon gwamna irin El-Rufai ya ƙaryata waɗannan sadaukarwa a kafar talabijin ta ƙasa, abin takaici ne kuma cin mutunci ga tunawa da jami’an tsaronmu,” in ji sanarwar.