Shugaban Sashen Ci gaban Koyon Ilimi na Kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano, Dr. Nafiu Sani Abas, ya bukaci gwamnatoci a matakai daban-daban da su mayar da hankali wajen fassara litattafan ilimi zuwa harshen Hausa domin taimaka wa ɗaliban Arewacin Najeriya su kara fahimtar darussa yadda ya kamata.
Dr. Nafiu ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce akwai gagarumin amfani a cikin fassara litattafan ilimi kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya.

Ya ce, “Idan aka dubi kasashen da suka ci gaba irin su China da Indiya, duk suna koyar da litattafan ilimi da harshensu na uwa. Wannan ba wai kawai yana kara fahimtar ɗalibai ba ne, har ma yana daga darajar harshensu a idon duniya.”
Shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Kano da su tabbatar da samar da dokar da za ta amince da amfani da harshen Hausa wajen koyarwa tun daga matakin firamare, sakandire har zuwa manyan makarantu a Arewacin kasar nan.
Ribado ya magantu Kan zargin da El-Rufai ya yiwa Gwamnatin tarayya game da yan bindiga
A cewarsa, akwai ƙwararrun malamai a jami’o’i da kwalejojin ilimi a Arewa da ke da kwarewar fassara litattafan kimiyya da ilimi irin su Physics, Chemistry, Biology da Ingilishi zuwa Hausa.
Ya bayyana cewa tuni sun kammala fassarar littafin Biology, kuma sun riga sun tura shi zuwa hukumar da ke da alhakin amincewa da buga littattafai ta kasa tare da ma’aikatar ilimi ta tarayya, inda ake jiran amincewa domin bugawa da rarrabawa a kasuwa.
Dr. Nafiu ya shawarci gwamnati ta bai wa wannan yunkuri cikakkiyar kulawa, yana mai cewa hakan zai taimaka matuka wajen bunkasa ilimin ɗaliban Arewacin Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu makwabta daga Kudu – musamman bangaren Yarbawa da Igbo – sun fara wannan tsari na fassara litattafan ilimi zuwa harshensu na uwa.
“A wannan matsayi ne ya dace mu a Arewa mu bai wa wannan tsari muhimmanci. Dole wakilanmu a majalisun dokoki su tallafa wa malamai masu wannan kwarewa domin a fassara litattafan ilimi zuwa Hausa, ta yadda ɗalibanmu za su rika karatu cikin harshensu na uwa,” in ji shi.
Daga karshe, ya ce kwalejin Sa’adatu Rimi na bude ga duk wata hadin gwiwa da gwamnati ko hukumomi za su bukata domin ganin an fassara litattafan ilimi zuwa Hausa, don a iya gogayya da kasashen da suka ci gaba, wadanda harshen uwa ya taka rawar gani wajen bunkasar su.