Wasu Matasa sun zargi Shugabar karamar hukumar Tudun Wada da yunkurin hallakansu ta hanyar amfani da yan daba

Date:

Wasu matasa dake sana’ar kire-kire a karamar hukumar Tudun Wada dake jihar kano sun zargi Shugabar karamar hukumar Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u da amfani da yan daba wajen far musu tare da ji musu raunita yayin da suke tsaka da gudanar da Sana’arsu.

Wata majiya ta ce matsalar ta samo asali ne daga rushe shagon da Matasan suke gudanar da sana’a wanda Hajiya Sa’a ta ba da umarnin a rushe domin gudanar da aikin wani titi da gina magudanar ruwa a yankin. Bayan kammala aikin ne kuma matasan suka koma bayan magudanar Ruwan da aka gina domin cigaba da sana’arsu, abin da daga bisani ya haifar da rikici tsakaninsu da shugabar karamar hukumar.

Guda Cikin Matasan Mustapha Bashir Tudun-Wada, wanda shi ma ya jikkata, ya shaida Kadaura24 cewa: “Muna zaune Muna aiki kawai muka ji mutane ne sun zo da Malamai suna dukan mu da Makaman har suka ji wa kusan mutane 7 daga cikin mu ciwo. Wannan abin da aka yi mana ba za mu yafe ba.”

Ya ce sun yi mamakin yadda aka zo aka far musu suna tsaka da gudanar da sana’arsu , Maimakon ita Shugabar karamar hukumar ta karfafesu amma sai ta buge da korarsu tare da sa yan daba su sassaresu.

Shi ma Ma’ud Tahir guda ne cikin wadanda suka jikkata ya ce ya cika da mamakin yadda shugabar Karamar Hukumar Tudun wada ta Jagoranci yan daba wajen Kai musu farmaki .

FB IMG 1753738820016
Talla

” An sare ni da adda kuma haka aka rika sararmu ni da abokan aikinna a lokacin da muke tsaka da aiki, bayan kuma a bayan ta rushe mana wajen sana’ar Amma har yanzu bata bar mu ba”.

Ya ce suna kira ga Gwamnan jihar Kano da hukumomin tsaro da su binciki Wannan lamari tare da daukar matakin da ya dace akan Shugabar karamar hukumar Tudun Wada Hajiya Sa’adatu Salisu don a tabbatar an yi musu adalci.

Matasan sun sha alwashin ganin an dauki mataki, tare da tabbatar da cewa ba za su bari irin wannan cin zarafi ya sake faruwa ba. Rahotanni sun tabbatar da cewa sun kai korafi ga rundunar ‘yan sandan Jihar Kano domin gudanar da bincike.

Kadaura24 ta tuntubi Shugabar karamar hukumar ta Tudun wada Hajiya Sa’adatu Salisu don Jin ta bakinta kan lamarin, Amma ba mu same ta a waya ba, mun kuma tura mata Sakon karya kwana Amma har lokacin hada Wannan Rahoton ba mu ji daga gareta ba.

Za mu cigaba da bibiyar Lamarin don Jin ta bakin ita shugabar hukumar da ake zargi da ɗauko yan daba su farma Matasan da suke gudanar da sana’arsu.

Al’ummar garin na jiran ganin yadda za a kammala batun, tare da neman ganin an samu adalci da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...

NUC ta kakabawa jami’o’i takunkumi kan yadda suke ba da digirin girmamawa a Najeriya

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta sanar...