Kungiyar ‘Yan Jarida Mata ta Najeriya (NAWOJ) ta yi tir da abin da ta kira cin zarafi da barazana ga tsohuwar shugabarta ta kasa, Comrade Ladi Bala, daga Daraktan Hukumar Sufurin Jirgin kasa ta Nigeria (NRC), Kayode Opeifa.
A cikin wata sanarwa da shugabar kungiyar ta kasa, Comrade Aisha Ibrahim, da sakatariyar ta kasa, Comrade Wasilah Ladan, suka rattaba wa hannu, kungiyar ta bukaci Daraktan ya fito fili ya bada hakuri ta hanyar wallafa sanarwar neman afuwa a jaridu fiye da guda daya, tare da yada shi a wata kafar rediyo ko talabijin.

NAWOJ ta kuma ce tun da cin zarafin ya shafi Hukumar Talabijin ta Kasa (NTA) inda Ladi Bala ke aiki, wajibi ne a kuma baiwa hukuma NTA hakuri .
Kungiyar ta bayyana cewa abin da ya faru barazana ce ga ‘yancin ‘yan jarida da tsaron su, lamarin da ta ce ba za ta lamunce shi ba.
NAWOJ ta zayyana bukatunta kamar haka:
Yin tir da cin zarafin da aka yi wa Ladi Bala wadda ta taba shugabantar kungiyar a matakin kasa.
Neman a bada hakuri a fili.
Daukar matakan da za su kare ‘yan jarida daga irin wannan cin zarafi a nan gaba.
Jaddada muhimmancin ‘yancin ‘yan jarida da tsaron lafiyarsu.
Kungiyar ta jaddada cewa kare lafiya da mutuncin ‘yan jarida shi ne babban abin da ya fi damunta, don haka ta bukaci Daraktan NRC ya gaggauta daukar matakin da ya dace.