Gamayyar kungiyoyin ci gaban yankin Kwaryar Bakin Kasuwa sun mika sakon godiya da jinjina ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewarsa da sanya fitilun titi a yankin — musamman a Zawiyar Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare Bari.
Kungiyoyin sun ce aikin ya zo a lokaci mai muhimmanci, ganin cewa ana shirye-shiryen gudanar da Mauludin Annabi (SAW) a zawiyar, inda fitilun za su taimaka wajen samar da haske da kuma inganta tsaro yayin taron.

Sun kuma bayyana farin cikinsu da yadda Gwamnan ya amince da bukatarsu cikin gaggawa da kulawa, abin da suka ce ya nuna irin yadda gwamnatinsa ke bai wa bukatun al’umma muhimmanci.
Kungiyoyin sun yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa Gwamna jagora tare da ba shi ikon cigaba da irin wadannan ayyuka na alheri.