Gwamnatin Kano ta kafa Kwamitin don bincikar Ganduje kan zargin sayar da mayanka

Date:

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamiti mai mambobi tara domin bincikar yadda mayankar dabbobi ta Chalawa, wacce aka gina shekaru sama da 35 da suka gabata, ta salwanta tare da dukkan kayan aikin da ke cikinta a zamanin gwamnatin baya.

Kwamitin wanda Barista Muhyi Magaji Rimin Gado zai jagoranta, ya kunshi wakilai daga sassa daban-daban na hukumomin gwamnati, inda aka ba su wa’adin makonni uku su gabatar da rahotonsu.

FB IMG 1753738820016
Talla

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, shi ne ya kaddamar da kwamitin a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ya bayyana cewa babban dalilin kafa kwamitin shi ne domin gano dalilan salwantar da katafaren ginin da aka yi da nufin bunkasa tattalin arzikin Kano.

NNPP ta bukaci INEC ta dakatar da zabuka

Ya ce daga cikin aikin kwamitin akwai bayar da shawara kan yadda za a gina sabuwar mayankar zamani da za ta dace da bukatu na yau wajen sarrafa nama. A cewarsa, yanzu haka kasashen Turai da Larabawa na da bukatar nama daga Kano, sai dai babu wannan cibiyar mai inganci da za ta taimaka wajen fitar da nama zuwa waje.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban kwamitin Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sakataren Gwamnati bisa amincewa da su. Ya tabbatar da cewa kwamitin zai yi aikinsa cikin gaskiya da rikon amana, ba tare da nuna son kai ko banbanci ba.

Rimin Gado ya kuma ce za su fadada binciken har zuwa jihohin makwabta domin gano ainihin dalilan da suka haddasa salwantar wannan muhimmiyar mayanka da aka gina da nufin inganta harkar noma da kiwo a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...