Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da ƙarin farashin yin fasafo wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025, domin inganta inganci da tsaro a tsarin fasafo ɗin ƙasar.
A cewar hukumar, farashin fasafo na shekaru biyar mai shafi 32 wanda a baya yake kan naira 70,000 yanzu zai tashi zuwa naira 100,000, yayin da na shekaru 10 mai shafi 64 wanda a baya yake kan naira 120,000 zai koma naira 200,000.

Sai dai, farashin fasafo da ‘yan Najeriya ke yi a ƙasashen waje ba zai canza ba, inda za a ci gaba da biyan dala 150 kan fasafo na shekara 5 da dala 230 kan fasafo na shekara 10.
Da dumi-dumi: Farfesa ya Zama Sakataren Ilimi na karamar Hukuma a Kano
Hukumar ta bayyana cewa wannan sabon tsarin na nufin tabbatar da daidaito a ayyukan fasafo, tare da sauƙaƙa damar samun fasafo ga duk ‘yan Najeriya