Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya amince da ƙarin mafi karancin albashi zuwa Naira 104,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar.
Uzodimma ya bayyana hakan ne a lokacin wata ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago a daren jiya Talata a fadar gwamnatin jihar da ke Owerri.

A cewar jaridar The PUNCH, kuma kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito, an kara mafi karancin albashin daga Naira dubu 76 zuwa Naira dubu 104.
Haka kuma, ya sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashi na likitoci daga Naira dubu 215 zuwa Naira dubu 503, yayin da na malamai a manyan makarantu ya karu daga Naira dubu 119 zuwa Naira 222 da sauran su.
Hisbah ta karɓi ƙorafe-ƙorafe sama da 83,000 a Kano
Ya ce ‘yan Jihar Imo sun fuskanci kalubale da dama tun bayan hawansa mulki, ciki har da matsalar tsaro, annobar COVID-19, matsin tattalin arziki sakamakon manufofin gyara, da rikici kan mafi karancin albashi da kuma cire tallafin man fetur.
Ya kara da cewa idan an biya ma’aikata albashi mai kyau, da a samu nagartar aiki, za a kyautatawa iyalai da saka su cikin farin ciki, kuma tattalin arzikin cikin gida ya na bunkasa.
Uzodimma ya bayyana cewa kudaden shiga na jihar (Internally Generated Revenue) sun karu daga Naira miliyan 400 zuwa sama da Naira biliyan 3 a kowane wata.