Gidan Radio Tarayya Pyramid FM Kano ya Sha alwashin hada hannu da Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano domin inganta harkokin tsaro a fadin jihar Kano.
” Za mu fara gabatar da wani shiri na tsawon awa guda kowanne sati domin ba ku dama ku shigo ku fadawa al’ummar jihar Kano Irin kokarin da kuke yi wajen Samar da tsaro da kuma wayar da kan al’umma yadda za su kaucewa aikata laifinn”.

Sabon Shugaban gidan Radio Dr. Garba Ubale Danbatta ne ya bayyana hakan yayin da Kaiwa Kwamishinan yansandan jihar Kano ziyara bangirma a ofishinsa .
Ya ce yansanda suna iya baki kokarinsu don ganin an sami ingantaccen tsaro a jihar Kano, a don haka akwai bukatar al’umma su ba su hadin kan da ya dace ta hanyar ba su bayanan sirri.
” Gidan Radio Pyramid yanzu ya dawo da karfinka domin tun daga zuwana na gudanar da aiyuka da dama wadanda suka kara karfin tashar ta yadda za a rika jinta a ko Ina a fadin jihar Kano da ma makwabtan Jihohi”. Inji Dr. Danbatta
Dr. Garba Ubale Danbatta ya kuma baiwa kwamishinan da duk Jami’an yansanda dake Kano tabbacin Pyramid Radio zata ba su dukkan wata gudunmawa da suke bukatar don kyautata harkokin tsaro a Kano .
Da yake nasa jawabin Kwamishina yansandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya yana saba da salon shugabancin Dr. Garba Ubale Danbatta saboda yadda ya Samar da cigaba a gidan Radio cikin kankanin lokaci .
” Tabbas kuna da muhummci a wajenmu saboda kune kuke sanar da al’umma kokarin da muke na Samar da tsaro, kuma muna fatan za ku cigaba da kokarin da kuke na wayar da kan al’umma kan muhimmcin tsaro”. Inji Kwamishinan
CP Ibrahim Bakori ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su cigaba da wayar da kan al’umma muhimmancin zaman lafiya ko za a sami raguwar aikata laifuka a jihar.