Hisbah ta karɓi ƙorafe-ƙorafe sama da 83,000 a Kano

Date:

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta ce a shekarar 2024 kaɗai ta karɓi ƙorafe-ƙorafe har 83,776, inda ta warware rikice-rikicen aure guda 621.

Hukumar ta kuma fasa dubban kwalaben giya bisa umarnin kotu, tare da karɓar sabbin mutane da suka rungumi addinin Musulunci.

Bugu da ƙari, rundunar ta ce ta tara kuɗaɗe da ta kuma raba a matsayin tallafi, kana ta karɓo kuɗin  bashi da aka gaza biya da ya kai naira biliyan 212,334,839.

FB IMG 1753738820016
Talla

Kwamandan rundunar, Sheikh Amin Ibrahim Daurawa, ya bayyana haka a Kano, inda ya ce tun bayan zuwan Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar 29 ga Mayu, 2023, an inganta harkokin Hisbah domin ƙarfafa ayyukanta.

Ayyukan da Hisbah ta gudanar

Sheikh Daurawa ya ce ayyukan da rundunar ta gudanar a cikin shekarar sun haɗa da:

Auren gata ga ma’aurata 3,800
Horon kara samun ƙwarewa ga jami’an Hisbah 1,000

Rabon kayan tallafi ga marayu, gwauraye da gajiyayyu.

Taimakawa masu aikin Hajji daga Kano zuwa Saudiyya.

A cewarsa, rundunar yanzu tana da jami’ai sama da 12,436 a kananan hukumomi 44 na jihar. Haka kuma akwai sashen mata karkashin jagorancin Dr. Khadija Sagir Suleiman, inda mata jami’ai suka kai 2,362.

Shirin gwamnatin Kano

Pyramid Radio zata hada hannu da Rundunar yansanda don inganta tsaro a Kano
Sheikh Daurawa ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin kafa:

Makarantar horar da jami’an Hisbah
Ƙara albashi da tsarin ritaya ga jami’an hukumar
Samar da sabbin kayan aiki
Gina sabuwar hedikwatar rundunar
Gwamnan ya jaddada cewa za su ci gaba da tallafawa Hisbah domin tabbatar da adalci, zaman lafiya da ɗorewar ɗabi’u masu kyau a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...