Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana da kudurin ganin rukunin gidajen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo sun kai matsayin na kasashen da suka cigaba .
Kwamishinan Raya Gidaje na jihar, Arc Ibrahim Yakubu Adamu ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi bakuncin wakilan Kungiyar Masu Gidaje da Mazauna Kwankwasiyya City da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.

A wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar Adamu Abdullahi ya aikowa Kadaura24 , ya ce kwamishinan ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kudurci aniyar ganin dukkan rukunin gidajen gwamnati da na yan kwangila da za a yi a Kano sun cika sharuddan da suka dace domin jin daɗin wadanda zasu mazauna cikinsu.
Kwamishinan ya ce gwamnati ta riga ta samar da muhimman abubuwan more rayuwa a cikin rukunonin gidajen, kamar ruwan sha mai tsafta, wutar lantarki, masallatai, makarantu da sauran abubuwa da ake bukata.
Ya kuma shawarci kungiyar ta karfafa wa mambobinta gwiwa wajen kammala gidajensu domin su zauna a ciki ko kuma su bayar da su haya, kamar yadda gwamnati ta bayar da sanarwa.
Cikakkun Hujjojin da Gwamna Kano ya Bayar Game da Zargin Karkatar da Kudi da ake wa Hadiminsa
Arc Adamu ya kara da cewa akwai korafe-korafe daga wasu da suka biya cikakken kudi amma aka basu gidajen da ba a kammala ba, inda ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi adalci a kan lamarin.
A nasa jawabin, shugaban riko na kungiyar, Alhaji Auwalu Inuwa Diso, ya gode wa gwamnati bisa yadda ta samar da yanayi mai kyau a cikin rukunonin gidajen .
Ya ce tun bayan sanarwar gwamnati kan kammala gine-gine, mutane da dama sun koma cikin gidajensu yayin da wasu suka bayar da nasu hayar. Sai dai ya roki gwamnati ta kara musu lokaci domin su samu damar cika sharuddan da ake bukata daga gare su.