Assalamu Alaikum.
Sanarwa ta musamman!
Gwamnatin jihar Kano na gargaɗi kan waɗanda ɓata garin matasa ke siyarwa da Rodika na slap, ƙarafunan futulun kan titi da wayoyin lantarki na gwamnati idan sun sace a kan tituna.
Mai girma gwamna Alhaji Abba K Yusuf, ya bada umarni na musamman ga ma’aikatar ayyuka ta jihar Kano, an janyo shugabannin masu harkar ƙarafuna na jihar Kano ana zaman tattaunawa da su dangane da matsalolin da suke faruwa musamman a kan sana’arsu, kwamitin ya haɗa da jami’an tsaro da sauransu.
“Idan har masu sana’ar ba sa siyan waɗancan kayayyaki na gwamnati to fa ba za su dinga zuwa su na sacewa ba, domin da yawan guraren da suke zuwa su farfashe slap ko wayoyin gwamnati da ƙarafuna ba ma aiki ne ya biyo ta wajen ba.
“Duk wanda aka riƙe ba zai ji da daɗi ba, yanzu daga ɓata garin matasan har waɗanda suke kawowa su siya an kafa tsatstsauran kwamiti wallahi duk wanda aka kama ba zai ji da daɗi ba!”.
“Iyaye, shugabannin unguwa da masu faɗa a ji su ja kunnen yayansu, yan kasuwa su guji siyan kayan da suka tabbatar daga hannun bata gari ya fito ko dukiyar gwamnati.

“Yanzu da wanda ya sato da wanda ya siya duk sunansu daya ne! “Barayi! Idan su ka kama mutum ba zai ji da daɗi ba!
Allah ya cigaba da daga martabar jihar Kano. Amin.
Engr. Marwan Ahmed
Hon. Commissioner
Ministry Of Works, Kano State.