Premier League: Sanata Barau zai daga darajar filin wasa na BUK

Date:

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, ya ce ya kammala dukkanin wasu Shirye-Shirye domin daga darajar filin wasa na Jami’ar Bayero Kano (BUK) a kokarinsa na bunkasa harkokin wasanni a Nigeria .

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a kwanakin baya ne kungiyar kwallon kafa ta Barau FC wadda mataimakin shugaban majalisar dattawa ya kafa ta samu karin girma inda za ta rika buga gasar firimiya ta Najeriya (NPFL).

FB IMG 1753738820016
Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa Sanata Barau Kan harkokin yada labarai Muddashir Isma’il ya aikowa Kadaura24 ranar talatar nan.

Sanarwar ta ce Sanata Barau ya bayyana Wannan kudirin na shi ne lokaci da wakilansa suka gana da Sabon shugaban jami’ar Bayero, inda shugaban ma’aikatan ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa Farfesa Muhammad Ibn Abdallah ya jagoranta

“Mai girma Sanata ya bukaci mu sanar da ku a hukumance kudirinsa na inganta filin wasan kwallon kafa na Wannan jami’ar ta yadda za a rika gudanar da wasannin kwallon kafa na kasa da sauran wasannin kwallon kafa a cikin”.

Muna kira ga INEC da ta sake duba sakamakon zaɓen Bagwai Da Shanono – Abdullahi Abbas

‘ Kamar yadda muka sani, ya gudanar da ayyuka da daman a Wannan jami’ar tare da kawo gine-gine don ciyar da jami’ar gaba, yanzu, ya ce BUK dole ne ta sami filin wasan ƙwallon ƙafa irin wanda ake amfani da shi a duniya don amfanar jami’ar, da al’ummarta da kuma sauran matasan mu,” inji shi.

Da yake nasa jawabin, shugaban majalisar ya godewa mataimakin shugaban majalisar dattawan bisa matakin da ya dauka na inganta filin wasan jami’ar.

“Mun yi farin ciki da samun wannan labari mai dadi, wannan wani bangare ne na tsarin da na mika wa Hukumar Gudanarwar Jami’ar nan cikin manufofinsa a lokacin da nake neman mukamin Shugaban wannan Jami’ar.

Ya ce ya jami’ar tana maraba da aikin sannan suna gode masa, sannan suna ba shi tabbacin ba shi dukkanin Hadin Kan da yake Bukata domin gudanar da aikin lami lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...