Jam’iyyar APC, reshen jihar Kano, ta bayyana cewa bata amince da sakamakon zaɓen cike gurbi na Dan Majalisar jihar da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, a mazabar Bagwai/Shanono.
“An samu maguɗi mai yawa, tashin hankali da tsoratar da masu kada kuri’a, tare da keta doka da oda gaba ɗaya, inda aka hana magoya bayan APC damar yin zaɓe cikin kwanciyar hankali, yayin da ’yan daba su ka yi abun da suke so a yayin zaben”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na jihar Kano Abdullahi Abbas ya sanyawa hannu kuma aka aikowa da Kadaura24.
APC ta jaddada cewa tsarin da aka bi bai cika ka’idodin zaɓe, gaskiya da adalci ba, tare da bayyana abin da ya faru a matsayin wani shiri na kwace ikon jama’a.
Dalilan da suka sa Kwankwaso ba zai hada hanya da Tinubu a zaben 2027 ba – Buba Galadima
Jam’iyyar ta yi kira ga hukumar zabe da ta gaggauta sake duba tsarin zaben da kuma sakamakon zaɓen, sannan ta na roƙon INEC da ta binciki rahotannin maguɗin da aka rika yadawa, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin dawowa da al’umma kwarin gwiwar cigaba da amincewar da tsarin zaben Kasar nan.