Daruruwan magoya bayan Jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya a Karamar Hukumar Bagwai sun roki gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf da kuma Shugaban Jam’iyyar na Jiha, Alh. Hashimu Suleiman Dungurawa su ceto Jam’iyyar daga hannun Jagororinta wadanda suka bayyana da cewa ‘yan jari hujja kuma ‘yan Kasuwar siyasa.
Magoya bayan Jam’iyyar sun bayyana hakan ne lokacin da suka yi cincirundon taya murna ga sabon Zababben Dan Majalisar Dokokin Jiha Mai wakiltar Kananan Hukumomin Bagwai da Shanono a gidansa dake garin Kiyawa Karamar Hukumar Bagwai, *Dr. Ali Lawan Alhassan Kiyawa*
Magoya bayan Jam’iyyar sun bayyana Jagororin nasu da cewa maciya amana ne babu abun da suka sani illa kawai yiwa Jam’iyyar zagon Kasa da almundaha tun a zaben 2023 har zuwa wannan zaben cike gurbin da aka gudanar a ranar asabar din da ta gabata.

Walilinmu dake wurin ya juyo yadda ake aibata Jagororin da muna nan kalamai lokacin da suka ziyarci gidan sabon Zababben Dan Majalisar inda har aka rika yi musu ihu da cewa bama so munafukai maciya amana.
Wasu daga cikin wadanda wakilin namu ya tattauna da su *Munkaila Idris Rimindako* da *Habibu Idris Wurabagga* sun bayyana cewa wadannan sune mutanen da suke hana ruwa gudu a matakin Karamar Hukumar tun lokacin da aka nada Shugabannin Kananan Hukumomi zuwa yanzu sun hana Shugaban Karamar Hukumar *Engr. Bello Abdullahi Gadanya* ya taimaki yan Jam’iyya da sauran mutane yadda ya kamata.
Sun bayyana cewa ko a wannan zaben da ya gabata duk kudaden da aka fitar don gudanar da harkokin zabe sun karbe sun kwashe abun da suka ga dama, wanda ba don taimakon Allah ba, da Jam’iyyar ta sake faduwa a wannan karon ma.
NNPP ta yi watsi da sakamakon Zaben Ghari da Tsanyawa a Kano
Masu korafin sun bayyana cewa wadannan Jagorori mafi yawancinsu sun fito ne daga mazabu biyu wato *Bagwai* da *Wurabagga* wadanda su ne manyan mazabu kuma duk manyan mukaman yankin suna wadannan mazabun kuma su kadai Shugaban Karamar Hukumar ya ke baiwa manyan kwangiloli amma kuma basa iya taimakawa ‘yan Jam’iyya, babban abun takaicin ma shine yadda wadannan Jagorori babu wanda ya iya kawo akwatunsa na zabe ballanta kuma mazabarsa a zaben da ya gabata.
Majiyar wakilin namu ta bayyana masa cewa su wadannan Jagorori da ake korafi akansu akalla babu wanda Shugaban Karamar Hukumar bai baiwa Kwangilar Naira milyan 20 zuwa fiye da Naira milyan 300 ba daga lokacin da aka zabi Shugaban Karamar Hukumar zuwa wannan lokaci amma taimako na Naira dubu 5 basa iya yiwa Kananan ‘Yan Jam’iyya sai dai su ce aje wajen Chairman ko kuma Shi sabon Zababben Dan Majalisar Dokokin, hatta a lokacin gangamin zaben, gwamna ya tambaya ana baiwa mata da matasa tallafin Naira dubu 50 kowane wata inda matasan suka shaidawa gwamnan cewa ba a basu, kuma sun zargi wadannan Jagororin musamman a Karamar Hukumar Bagwai da karkatar da wadannan kudade ga iyalansu kawai, sai dai gwamnan ya ce zai bincika.
Wani Kansilan mazaba da ya nemi a sakaya sunansa ya ce hatta su kansu Kansiloli wadannan Jagorori sun hana Shugaban Karamar Hukumar ya taimake su, sai dai duk abun da Kansila yake so, na aiki sai dai a sammasa abun da bai fice cikin lokaci ba, wanda Shi kansa babu yadda zai yi ya taimaki wani Dan Jam’iyya na Kasa, wanda yace wannan dalilin ne yasa da dama ‘Yan Jam’iyyar suka ki zabar Jam’iyyar musamman a wadannan mazabu da aka ambata, don haka yace ya zama wajibi Jagorori daga matakin Jiha sai sun shiga wannan lamari domin ceto Jam’iyyar daga hannun wadannan mutane da kuma yiwa Shugaban Karamar Hukumar gargadi akan yadda yaki fuskantar kowa sai su kadai duk da cewa yana bakin kokarinsa wajen taimakawa ‘Yan Jam’iyya da Shi da sabon Dan Majalisar da aka zaba.
Wakilin namu ya gano cewa Jagororin da ake zargi da wannan almundahana da kuma baba kere sun hada da Shugaban Jam’iyyar na Karamar Hukuma *Alh. Mas’ud Badau* wanda aka ce kuri’a daya tal ya samu a akwatunsa a wannan zaben cike gurbin duk da kuma zargin cewa sai da ya kwashe Naira dubu 600 daga cikin kudaden agent na Jam’iyyar da sauran kudaden ayyukan Jam’iyya na mazabar Wurabagga a daren Juma’a ana gobe zabe, sai Shugaban Kwamitin Dattawa *Alh. Musa Ibrahim Kasco* shima mutumin Badau ne Mazabar Wurabagga wanda aka kiyasta akalla yanzu haka yana yin kwangiloli na fiye da Naira milyan 500 a sassa daban daban na Karamar Hukumar amma Naira dubu 5 baya iya bayarwa a matsayin taimako ga Kananan ‘yan Jam’iyya wanda haka tasa shima aka kayar da Shi a akwatunsa na zabe, sai kuma Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar *Haruna Garba Bagwai* wanda aka yiwa lakabi da *Sarkin Biro* wanda shima ya sha kaye a akwatunsa da kyakkyawan rinjaye saboda tsabagen rowa da mugunta wanda shima a yanzu haka an ce Shugaban Karamar Hukumar ya ba Shi kwangilar gyaran gidan Hakimin Bagwai akan Naira kusan milyan 100 ban da sauran kwangiloli da yake a sauran wuraren.
Sauran wadanda magoyan bayan Jam’iyyar ta NNPP a Bagwai suke korafin sun kasa cin akwatunansu a zaben da ya gabata da sauran zabubbuka na baya sun hada da Jagoran Jam’iyyar gaba daya *Alh. Salisu Garba Bagwai* wanda tsohon Darakta ne a Hukumar NOA ta Kasa reshen Jihar Kano sai tsohon mataimakin Shugaban Karamar Hukumar kuma Shugaban mazabar Bagwai a yanzu *Faruk Aliyu Bagwai* da Kansilar walwalar Jama’a *Hajiya Balaraba Lawan Bagwai* sai Mataimakin Jagoran Jam’iyyar *Alh. Sa’idu Garba Sarkin ‘Ya* sai Sakataren ilmin Karamar Hukumar *Malam Mustapha Lawan Majingini*
sai Shugaban Kansilolin yankin *Hon. Sani Ibrahim Badau* wanda akwatunsu daya da Shugaban Caucus da Kwamandan Hisba *Isah Idris Badau* da kuma Jami’in alhazan yankin wato Centre Officer *Bello M. Abdullahi* duk wadannan sune ake zargi da rashin tabuga wani abun kirki a akwatunansu da mazaba har Jam’iyyar ta fadi, sai dai shi Jami’in alhazai wato Centre Officer *Bello M. Abdullahi* ana ganin akwai saukin zargin gazawa a kan sa saboda kayen da Jam’iyyar APC ta yi masa a akwatunsa kalilan ne bai wuce kuri’a 20 ba domin ance ya dara sauran Jagororin yiwa ‘Yan Jam’iyya hidima, sannan an yi ittifakin cewa baya cikin wadanda suka taba amfana da kwangilolin ayyuka da Shugaban Karamar Hukumar ya ke baiwa sauran Jagororin Jam’iyyar a yankin.
Dama dai wadannan su ne manyan mazabu a Karamar Hukumar Bagwai da Wurabagga kuma su ne suke da dukkan masu rike da manyan Mukamai a matakin Karamar Hukumar amma kuma su ne koda yaushe Jam’iyyar ke shan kaye daga hannun Jam’iyyar APC in banda shigowar tsohon Dan Majalisar Dokokin Jihar *Hon. Ado Isyaku Daddauda* wanda ya sake dawowa cikin Jam’iyyar kasa da kwanaki 30 wanda ya yi namijin kokari wajen kawo dukkan akwatu nan garinsu Daddauda guda 8 tare da gagarumin rinjaye wanda hakan ya sanya kayen da aka yiwa Jam’iyyar NNPP a mazabar Bagwai bai wuce kuri’a 15 ba, amma dukkan akwatu nan dake cikin garin Bagwai guda 21 Jam’iyyar APC ce ta cinye su baki daya.
Sai dai kuma wata matsalar da walilinmu ya gano na kayen da Jam’iyyar NNPP ta sha a cikin garin ba ya rasa nasaba da kwace takara da aka yi daga hannun wanda ya yiwa Jam’iyyar NNPP takara a zaben 2023 *Hon. Ahmad Musa* domin ya fito ne daga cikin garin Bagwai duk da cewa ya lallashi magoya bayansa su zabi Jam’iyyar.
Yanzu dai magoya baya suna jiran Jagororin Jam’iyyar a matakin Jiha su ga hukunci da kuma matakin da zasu dauka akan wadanda magoya bayan Jam’iyyar suka zarga da cin amana da kuma almundahana a yankin.