Al’ummar Bagwai/Shanono da kungiyoyin fararen hula sun koka kan tashin hankali, tsoratarwa da tauye wa masu kada kuri’a ‘yancinsu

Date:

Daga Nasiru Waziri.

Hadakar Kungiyoyin Fararen Hula (CSO’s) tare da al’ummomin Bagwai/Shanono sun bayyana damuwarsu cewa zaben ya kasance cike da tashin hankali, tsoratarwa, da kuma tauye wa masu kada kuri’a hakkinsu.

Wannan na kunshe ne cikin jawabin da Farfa M. D. Muktar ya gabatar a madadin CSO’s da suka kasance cikin masu sa ido a zaben cike gurbi na Majalisar Jiha a Bagwai/Shanono da aka gudanar a ranar 19/08/2025.

 

A iya tunawa, Cibiyar Gudanar da Rikice-Rikicen Dabaru (Center for Strategic Conflict Management), wacce INEC ta amince da ita a matsayin mai lura da zabe, ta fitar da rahoton wucin gadi kan zaben cike gurbi na majalisar jiha da aka gudanar a Bagwai/Shanono a ranar 16 ga watan Agusta, 2025.

A cewar rahoton, zaben ya kasance cike da tashin hankali, tsoratarwa da kuma tauye hakkin masu kada kuri’a.

Wani ganau wanda ya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa “yan daba dauke da makamai” masu sanya rawanin ja sun rika yawo suna tsoratar da masu kada kuri’a tare da kawo cikas ga gudanar da zaben.

 

FB IMG 1753738820016
Talla

Ya kara da cewa, an kori masu kada kuri’a daga rumfunan zabe, inda da dama suka tsere saboda tsoron rauni.

Rahoton ya kuma nuna cewa makarantar kayan zabe ta yi jinkirin zuwa, abin da ya kara dagula gudanar da kada kuri’a.

Prof. M. D. Muktar ya bayyana cewa fiye da dari na yan daba dauke da makamai masu hadari an cafke su.

Bugu da kari, manyan jam’iyyun siyasa da suka hada da ADC, APC, da PDP, duk sun la’anci tashin hankalin da aka tafka tare da yin kira ga gudanar da bincike da soke sakamakon zaben.

A cikin rahotonsa, Cibiyar Gudanar da Rikice-Rikicen Dabaru ta ba da shawara cewa jam’iyyun siyasa su wayar da kan mambobinsu kan yadda ake gudanar da dimokuradiyya.

Muna kira ga INEC da ta sake duba sakamakon zaɓen Bagwai Da Shanono – Abdullahi Abbas

Haka kuma, duk wanda aka samu da laifin karya doka a zabe dole a hukunta shi yadda ya dace, domin tabbatar da samun sahihin, adali, kuma ingantaccen zabe, wanda shi ne ginshikin dimokuradiyya.

Prof. M. D. Muktar ya jaddada cewa tawagar masu lura da zabe sun kammala da cewa a Shanono babu wani zabe da aka gudanar, suna bayyana tsarin gaba daya a matsayin “wasa da rashin gaskiya”. Saboda haka suna kira da a soke zaben gaba daya domin gazawarsa wajen cika ka’idojin da ake bukata na gudanar da zabe a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nan gaba kadan za mu bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya – Babban Hafsan tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce...

Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano

Gwamnatin Jihar Kano Hadin gwaiwa da Rundunar Yansandan Jihar...

Masu Mukamai a gwamnatin Kano ba su da uzurin kin taimakawa yan Kwankwasiyya – Sanusi Bature

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin...

Magoya bayan Barr Ibrahim Isa (Matawallen Gwagwarwa) sun aikawa Gwamnan Kano Budaddiyar Wasika

Daga Isa Ahmad Getso Kira don nemawa Barr. Ibrahim Isa...