Dalilan da suka sa Kwankwaso ba zai hada hanya da Tinubu a zaben 2027 ba – Buba Galadima

Date:

Guda cikin jiga-jigan jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya ce jagoran jam’iyyar tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba zai taimakawa shugaban kasa Bola Tinubu ba don ya sake lashe zabe a 2027.

FB IMG 1753738820016
Talla

Galadima, wanda ya kasance bako a shirin Siyasar Yau na Gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, ya ce Shugabancin Tinubu ya yi wa Kwankwaso da Jam’iyyar NNPP mugun nufi a Kano ta hanyar mara wa hambararren Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero baya, duk kuwa da tsige shi da Gwamna Abba Kabir na NNPP ya yi.

“Ta yaya Kwankwaso zai zama abokin APC da abin da suke yi mana a Kano, nada sarakuna biyu a gari daya, akwai Sarkin Gwamnatin Tarayya da Sarkin Jiha, wane ne ke da alhakin nada sarakuna da biyansu albashi?

Galadima ya yi alfahari da cewa NNPP ce za ta yanke hukunci kan shugaban Najeriya a 2027. “Mu ne mutanen da za su tantance wanda zai zama shugaban Najeriya a 2027,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...

NUC ta kakabawa jami’o’i takunkumi kan yadda suke ba da digirin girmamawa a Najeriya

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta sanar...

Tsoffin Kwamishinonin Kano sun Musanta labarin goyon bayan Sanata Barau a 2027

Kungiya ta tsoffin kwamishinoni da suka yi aiki a...