Zabe:An kama ƴandaba sama da 100 da ake zargi da yunkurin tada tarzoma a Kano – INEC

Date:

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa an kama fiye da mutane da ake zargin ƴandaba ne sama da ɗari, yayin da jami’an tsaro su ka yi nasarar dakile yunkurinsu na tada hargitsi a zaɓen cike gurbi na majalisar jiha a mazabar Bagwai/Shanono da ke jihar Kano.

Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Ambasada  Abdul A Zango ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ƴan jarida kan yadda ake gudanar da zaɓen a karamar hukumar Bagwai a yau Asabar.

FB IMG 1753738820016
Talla

A cewarsa, rundunar ƴansanda ta tabbatar masa cewa an kama fiye da ƴandaba 100 kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

“An kama fiye da ɗari. Ƴansanda sun tabbatar mana. Ku ma kun gani da idonku. Tsarin yana ci gaba kuma za a gurfanar da su,” in ji shi.

Gwamnati da Malamai a Kano sun fitar da mafi karanci kudin sadaki da Zakka da Diyar Rai

Abdu ya ƙara da cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali domin babu wani rahoton tashin hankali da aka samu har zuwa yanzu, yana mai yabawa da yadda aka samar da tsaro a wuraren.

“Ina matuƙar jin daɗi, musamman yadda aka tsara tsaro, an tura jami’an tsaro da dama tare da sintiri. An dakile dukkan ’yan daban, an kwantar da su. Tsarin yana tafiya lafiya lau, lallai na yi matuƙar gamsuwa,” in ji shi.

IMG 20250802 WA0088(1)
Talla

Kwamishinan ya bayyana cewa yawancin wuraren zaɓe sun fara gudanar da aikin tun da karfe 8:30 na safe.

Sai dai ya ce an samu ɗan jinkiri a wurare kaɗan sakamakon lalacewar wasu motocin da ke ɗauke da kayan zaɓe da jami’ai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

PDP ta yi watsi da zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono dake Kano

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya...

Jam’iyyar APC ta bayyana matsayarta kan zaben cike gurbi a Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Gwamnan Bauchi ya nada ɗan ƙasar China a matsayin mai bashi shawara kan tattalin arziƙi

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nada Mista Li...

Gwamnati da Malamai a Kano sun fitar da mafi karanci kudin sadaki da Zakka da Diyar Rai

Daga Kamal Yakubu Ali   Hukumar Zakka da Hubusi da Takwararta...