Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe ta dakatar tare da soke zaɓen cike gurbi da ke gudana yanzu haka a jihar Kano saboda “tashin hankali”.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce ‘”‘yandaba sun tarwatsa kayayyakin zaɓe a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da Gari”, inda ake gudanar da zaɓen ɗanmajalisar tarayya.
A cewarta: “Cigaba da kaɗa ƙuri’a a irin wannan yanayin na dabanci da tilasta wa masu zaɓe ya saɓa da tanadin dimokuraɗiyya na gudanar da sahihin zaɓe, kuma zai koyar da satar ƙuri’a da ba za a yarda da shi ba,” in ji sanarwar.

Duk da cewa APC ce riƙe da mulkin a tarayya, NNPP ce mai mulki a jihar ta Kano da ke arewacin ƙasar.
Zuwa yanzu ba a kai ga samun sakamakon zaɓen a hukumance ba, yayin da ake ci gaba da kaɗa ƙuri’a a wasu rumfunan zaɓen.