Gwamnati da Malamai a Kano sun fitar da mafi karanci kudin sadaki da Zakka da Diyar Rai

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Hukumar Zakka da Hubusi da Takwararta ta Shari’a da majalisar Malamai da kungiyar limaman masallatan juma’a ta jihar Kano sun fitar da matsaya akan abun da ya shafi Nisabin Zakka, Diyyar Rai Da Sadakin Aure a fadin jihar Kano.

Yayin zaman kowanne bangaren ya amince da Naira dubu asirin (20,000.00) a matsayin mafi karancin Nisabin Sadakin Aure a fadin jihar Kano.

Haka kuma sun amince da Naira miliyan dari da hamsin (150,000,000.00) a matsayin Diyyar wanda ya kashe Rai bisa kuskure da kuma naira dubu Dari tara da tamanin da biyar (985,000.00) a matsayin Nisabin Zakka.

FB IMG 1753738820016
Talla

Farfesa Aliyu Tahiru Muhammad, Malami a Jami’ar Bayero dake Kano kuma babban Sakataren kungiyar masu aikin Zakka da wakafi ta kasa ne ya bayyana hakan a jawabin bayan taro da hukumar Shari’a ta Jihar Kano da Takwararta ta Zakka da Hubusi da shugabancin kungiyar Limaman masallatan juma’a da majalisar Malamai ta Jihar Kano da kungiyar ma’aikatan Zakka da wakafi ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar.

“Abubuwan da aka amince da su a wannan taro sune kamar haka;

1. Taron ya amince da amfani da Durham a matsayin ma’aunin nisabin Zakka a jihar Kano wanda Kimarsa ta kai naira dubu Dari tara da tamanin da biyar a yau.

Rundunar yan sanda ta Sanya dokar takaita zurga-zurga a wasu kananan hukumomi a kano

2. Zaman ya amince da cewa Sadaki yarjejeniya ce tsakanin waliyan yarinya da wakilan Ango wanda za su yi la’akari da wadatar mai Aure da Kimar wacce za’a aura da halin da ake ciki, amma duk yarjejeniyar da za su yi ka da sadakin ya gaza naira dubu asirin.

3. Diyyar Rai ta kama naira miliyan dari da hamsin. Amma ga wanda ya yi kisan ganganci, za’a koma ga mataki mafi tsauri, wanda Alkali zai fitar da shi a wajen yin hukunci.

4. Za’a rika yin wannan zama duk bayan wata uku domin yin duba ga wannan batutuwa.

IMG 20250802 WA0088(1)
Talla

5. Za’a sanar da gwamnatin wacce zata kirawo taron wayar da kai da na ‘yan Jaridu da kuma isarwa ta hanyar da duk ta dace. Hakazalika suma sauran majalisar Malamai da hukumomin da abin ya shafa za su taimaka wajen isar da sakon.

Tunda farko, shugaban hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano Barista Habibu Muhammad Dan-Almajiri ya ce daukar matakin ya biyo bayan yadda a lokuta daban-daban Malamai ke bada mabanbantan Bafawoyi game da nisabin zakka da sadaki da biyan Diyyar Rai.

Dan-Almajiri ya yi fatan Malamai a fadin Jihar Kano za su taimaka wajen dabbaka matsayar da aka cimma.

Taron ya samu halartar manya malamai da dama da suka hadar da farfesa Ahmed murtala daga jami’ar Bayero, da farfesa Ibrahim mai Bushira shi ma daga jami’ar Bayero sai Sheikh Ibrahim Sheikh Maihula da Sheikh Abdullahi Uwaisu Limanci da Gwani Hadi da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Jam’iyyar APC ta bayyana matsayarta kan zaben cike gurbi a Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zabe:An kama ƴandaba sama da 100 da ake zargi da yunkurin tada tarzoma a Kano – INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta...

Gwamnan Bauchi ya nada ɗan ƙasar China a matsayin mai bashi shawara kan tattalin arziƙi

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nada Mista Li...

Rundunar yan sanda ta Sanya dokar takaita zurga-zurga a wasu kananan hukumomi a kano

Daga Isa Ahmad Getso   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...