Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nada Mista Li Zhensheng, ɗan ƙasar China, a matsayin mai ba da shawara kan tattalin arziƙin jihar.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an sanar da hakan ne yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar da cibiyar China Global Promotion Cooperation Research Centre.
Gwamnati da Malamai a Kano sun fitar da mafi karanci kudin sadaki da Zakka da Diyar Rai
Yarjejeniyar na nufin haɓaka zuba jari, bunƙasa gine-gine, da haɗin kai a fannoni kamar noma, ilimi, kiwon lafiya, masana’antu, hakar ma’adinai, da kasuwanci.
Za a kuma buɗe ofishin wakilan Bauchi a ƙasar China domin sa ido kan aiwatar da ayyuka.

Gwamna Bala ya ce haɗin gwiwar ta dace da manufofin diflomasiyya tsakanin shugabannin ƙasashen Najeriya da China, kuma za ta taimaka wajen samar da ayyukan yi, haɓaka ƙwarewa, da ƙara wa Bauchi suna a duniya.
Mista Zhensheng ya yi alƙawarin kawo goyon bayan cibiyarsa domin ci gaba mai ɗorewa a jihar.