Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Rano Alhaji Naziru Ya’u na tsawon watanni uku sakamakon rashin Iya tafiyar da mulki da karya dokokin aiki tare da umartar sa ya mika aiki ga mataimakin sa.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne yayin zaman da ta gudanar a Wannan Rana ta Laraba.
Wata Majiya ta shaidana cewa an dauki matakin ne saboda zargin Shugaban karamar hukumar da sayar da tsohuwar kasuwar Rano.
Rahotanni dai sun nuna cewa ana zargin Shugaban karamar hukumar da aka dakatar da sayar da takin zamani ko karkatar da shi wanda gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rabawa kananan hukumomin kano a watan Yulin da ya gabata.
Ko wacce karamar hukuma ta samu tirela uku na takin zamanin mai dauke da buhu 600 ko wacce mota

Haka kuma Majalisar ta yi karatu na daya akan kudirin dokar kwarya kwaryar kasafin kudi na wannan shekarar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata wanda yakai fiye da naira biliyan dari da sittin da tara.
Gwamnan Kano ya Gabatarwa Majalisar Dokokin Jihar Wasu Manyan Bukatu
Akawun majalisar Alhaji Bashir Idris Diso shine yayi karatun a yayin zaman majalissar na yau laraba.

Zaman majalissar Wanda shugaban ta Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jagoranta ya amince Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Alhaji Sa’id Yahaya a matsayin shugaban hukumar karbar korafi da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Hakan ya biyo bayan rahoton da shugaban kwamitin karbar kirafi na majalissar kuma dan Majalissa mai wakiltar karamar hukumar Dala Alhaji Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ya gabatar.
Ya ce Alhaji Sa’id Yahaya ya cika dukkanin Ka’idojin da doka ta tanadar kafin nada mutum a matsayin shugaban hukumar.