Kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya (NAWOJ), reshen jihar Kano, ta jaddada kudirinta na ganin ana Sanya mata a matakan shugabanci don su ba da ta su gudunmawar wajen kawo cigaba ga al’umma.
Da take jawabi a wajen wani taron karawa juna sani na yini gudu shugabar kungiyar Kwamared Bahijja Kabara ta jaddada cewa dole ne a baiwa mata ‘yancin bayar da gudunmuwarsu don kawo ci gaba ga al’umma.

Taron wanda aka shirya tare da hadin guiwar gidauniyar Aminu Magashi da kungiyar kula da lafiya da bincike ta al’umma, an shirya shi ne domin kara karfafa gwiwar mata ‘yan jarida wajen bayar da rahotanni na hakika kuma a kan lokaci, tare da magance kalubalen da suke fuskanta a cikin gida da ma duniya baki daya.
Gwamnan Kano ya raba tallafin kayan sana’o’i ga matasa 1130
Bahijja Kabara ta bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu don ciyar da aikinsu gaba da kuma muradun mata.
Ta yabawa gidauniyar Aminu Magashi bisa jajircewa da take yi wajen kula da lafiyar mata da yara, da kuma jin dadin al’umma, inda ta bayyana gidauniyar wacce za su cigaba da hada Kai tsare- don cigaban al’umma.

Kabara ya kuma yabawa Shugaban kungiyar NUJ na jihar Kano Kwamared Sulaiman Abdullahi Dederi bisa jagorancinsa na ci gaba da kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake ba da fifiko ga ci gaban mata musamman ta hanyar samar da dokar da kula da mata masu juna biyu kyauta.