Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba tallafin kayan sana’a ga matasa 1130 da aka yaye a makarantun koyar da sana’o’i shida da gwamnati ta bude.
Da yake jawabi a wajen rabon kayan tallafin a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf yace gwamnatinsa ta himmatu wajen samarwa matasa ayyukan yi domin su dogara da kawunansu.

Daliban su 1130 sun fito ne daga makarantar koyar da kiwon Kifi data koyar da ilimin kwamfuta data koyar da kiwon dabbobi data koyar da ilimin kula da tssirrai data koyar da tukin mota da kuma ta koyar da wasan kwaikwayo.
Da yake jawabi ga matasan da aka yaye gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ta bawa daliban kwalejin nazarin ilimin kwamputa laptop da kunshin kayan gyaran computer da wayoyin hannu da kuma kudi naira dubu hamsin.
2027: Tsohon SSG Na Kaduna Ya Shawarci Sha’ban Ya Bar APC Ya Shiga ADC Don Yin Takarar Gwamna
Sai na ma makarantar koyon kiwon dabbobi wadanda suka samu tallafin shanu yayin da na makarantar koyon tukin mota suka rabauta da shaidar tuki (Driving licence) da kuma kudi Naira dubu 100 kowannensu.

Daliban kwalejin nazarin ilimin tsirrra kuwa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya gwangwaje su da kayan aikin noma da tallafin kudi yayin da na makarantar koyon wasan kwaikwayo suka rabauta da camerar daukar hoto ta zamani da kuma kudi Naira dubu 50.
Ya yi kira ga matasan suyi kyakkyawan amfani da tallafin da kuma ilimin da suka Koya Yadda ya dace.