Daga Rahama Umar Kwaru
Wani bidiyo da ya fara yawo a shafukan sada zumunta ya nuna tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna a zamanin tsohon gwamna Malam Nasir El-Rufai, Hon. Bashir Sa’idu, yana kira ga tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon. Sani Sha’ban, da ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar haɗaka ADC.
An jiyo Hon. Bashir yana yin kiran ne yayin da suke gaisawa da Hon. Sha’ban a wajen wani ɗaurin aure da suka halarta a garin Zariya, ranar Asabar 9 ga watan Agusta, 2025.
A cikin tattaunawar, Bashir ya ce:“Ina ba ka shawara ka bar APC. Mun san irin yaudarar da suke yi maka da alkawurran bogi na mukami da har yanzu ba su cika ba. Wannan dai halayya ce ta yawancin shugabannin APC, musamman gwamnan Kaduna.

Ka shigo ADC, mu ba ka tikitin takarar gwamna kai tsaye. Kai fitaccen ɗan siyasa ne mai jajircewa da tarin jama’a tun daga tushe.”
Bashir ya kara da cewa babu wani abin amfani da APC za ta iya yi wa Sha’ban, “domin tuni abin da suke da shi sun yi maka.”
Kokarin da manema labarai suka yi don jin ta bakin Hon. Sha’ban ya ci tura, sai dai wani daga cikin magoya bayansa ya ce ba shi da ikon cewa komai akan lamarin har sai daga bakin ɗan siyasan.
Belin Dilan Kwaya: Gwamnan Kano ya kori wasu Hadimansa
Sai dai wata majiya daga cikin makusantan Sha’ban ta shaida wa manema labarai cewa, magoya bayansa tun tuni suke koka kan wariyar da ake nuna masa a APC. Ta kara da cewa:
“Kowa ya san akwai kyakkyawar alaka tsakanin Sha’ban da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, Kakakin Majalisar Tarayya Tajudeen Abbas, da kuma gwamna Uba Sani. Muna rokon jama’a su ci gaba da yi masa addu’a, Allah ya zaba masa abin da ya fi alheri.”

Idan za a iya tunawa, Hon. Sha’ban ya tsaya takarar gwamna a karkashin ACN a shekarar 2011, daga bisani ya jagoranci kafa jam’iyyar APC a 2015. A 2023 ya sauya sheka daga APC zuwa ADP, inda ya tsaya takarar gwamna, kafin daga baya ya sake komawa APC a ƙarƙashin gwamna Uba Sani.
A yanzu, ana ci gaba da sa ido kan matakin da zai dauka.