Daga Jafar Adam
Allah ya yiwa Kanal Daudu Sulaiman Rasuwar a Wannan Rana ta Asabar
Guda cikin yayan Marigayin Umar Daudu Sulaiman ne ya tabbatarwa da Kadaura24 rasuwa.
Kanal daudu Sulaiman tsohon Sojan Nigeria ne da ya ba da gagarumar gudunmawa wajen Hadin Kan Nigeria .

An haife shi a garin Bebeji dake jihar Kano 17 Disamba 1942.
Belin Dilan Kwaya: Gwamnan Kano ya kori wasu Hadimansa
Ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a kasar masar . Ya rasu ya bar ya’yan 8 da jikoki da dama.
Nan gana za a sanar da lokacin da za a yi jana’izarsa .